Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-16 08:41:31    
Ganawa tsakanin shugaban kasar Malawi da Yang Jiechi

cri

A ran 15 ga wata, shugaban kasar Malawi Bingu Wa Mutharika ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi a birnin Blantyre.

Mutharika ya ce, a cikin shekara daya da aka kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Malawi, an yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a karkashen dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda ya bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma. Gwamnatin Malawi ta tsaya tsayin daka a kan manufar Sin daya tak. Tana fatan kasashen biyu za su kara yin mu'amala tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kara hadin gwiwa don samun moriyar juna, ta haka za a kara samun nasarori da yawa.

Yang Jiechi ya ce, tun lokacin da aka kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, an kara samun amincewar juna tsakanin bangarorin biyu a fannin siyasa, shugabannin kasashen biyu sun cimma daidaito kan raya dangantaka tsakaninsu, wanda ya inganta dangantakarsu. Ya nuna yabo ga gwamnatin Malawi da ta tsaya tsayin daka a kan manufar Sin daya tak da nuna goyon baya ga Sin kan manyan batutuwa kamar gasar wasannin Olympics ta Beijing. Bangaren Sin yana fatan yin kokari tare da bangaren Malawi wajen raya dangantaka tsakaninsu lami lafiya.

A wannan rana, Yang Jiechi ya yi shawarwari tare da takwara aikinsa na Malawi Joyce Banda a babban birnin kasar. Bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su yi kokari tare don ciyar da dangantaka tsakanin kasashen biyu gaba.(Zainab)