Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-15 14:21:01    
Ganawa tsakanin shugaban kasar Ruwanda da Yang Jiechi

cri

A ran 14 ga wata, shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi a babban birnin kasar.

Kagame ya ce, an samu cigaba wajen dangantaka tsakanin kasashen Ruwanda da Sin a cikin shekarun da suka wuce, kuma an yi hadin gwiwa mai kyau a fannoni daban daban. Kasar Sin ta nuna goyon baya da ba da gudummawa wajen raya kasar Ruwanda, sabo da haka bangaren Ruwanda ya nuna godiya ga kasar Sin.

Kagame ya yabawa dangantakar hadin gwiwa da sada zumunci tsakanin Sin da kasashen Afirka sosai. Ya ce, tun lokacin da aka kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, an samu nasarori da yawa wajen hadin gwiwarsu, kuma dandalin ya taka muhimmiyar rawa wajen raya kasashen Afirka. Kasar Ruwanda tana son yin kokari wajen inganta dandalin da raya dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Yang Jiechi ya ce, kasashen Sin da Ruwanda suna da zumunci mai zurfi. Game da tinkarar rikicin hada-hadar kudi, kara hadin gwiwa tsakaninsu zai ba da taimako wajen kiyaye bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma.

Yang Jiechi ya ce, kasar Sin na dora muhimmanci kan dangantakar hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka, kuma za ta yi hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, da gudanar da ayyukan da aka tsara a taron koli na Beijing na dandanlin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, musamman matakai takwas na kara hadin gwiwa tsakaninsu don ingiza dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.(Zainab)