Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-14 09:01:18    
Shugaban kasar Uganda ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi

cri

A ranar 13 ga wata, a birnin Entebbe, shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi wanda ke yin ziyara a kasarsa.

Museveni ya yaba da dangantakar da ke tsakanin Uganda da Sin. Ya bayyana cewa, tun shekaru da dama da suka wuce, kasashen biyu sun sami amincewar juna tare da nuna wa juna goyon baya wajen harkokin siyasa, kuma sun yi hadin gwiwa kan tattalin arziki da cinikayya da sha'anin gona da manyan ayyuka da dai sauran fannoni. Yana fatan kasashen biyu za su kara inganta hadin gwiwa tsakanin manyan jami'ansu kuma su kara hada kansu a kan batutuwan duniya, don kara zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu daga dukkan fannoni, da ingiza dangantakar da ke tsakaninsu.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya dora muhimmanci sosai kan dangantakar sada zumunci tsakanin Sin da Uganda, yana fatan inganta mu'amala tare da bangaren kasar Uganda, don kara karfafa hadin gwiwa ta moriyar juna tsakaninsu, ta yadda za a iya kara ingiza dangantakar sada zumunci tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kira taron koli na Beijing na daddalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, kuma a karkashin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, an gudanar da matakan da aka cimmawa a gun taron kamar yadda ya kamata. Alal misali, an gudanar da manufofi 8 na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika lami lafiya. Bangaren kasar Sin yana son kokarin tare da kasashen Afrika ciki har da Uganda, don ciyar da sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afrika, ta yadda za a iya kara kawo moriyar jama'ar kasashen biyu.(Bako)