A kwanakin nan, wasu masana da jami'an Afirka sun yi hira da 'yan jaridu, sun ce, bayan da kasar Sin ta gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, tattalin arzikin zaman al'umma ya sami bunkasuwa da sauri, kuma Afirka za ta iya yin amfani da fasahohin Sin da yin hadin gwiwa tare da Sin a duk fannoni don kawar da talauci.
Wani mashahurin marubucin kasar Mali Seydou Bodian ya ba da shawara cewa, kamata ya yi Afirka ta yi koyi da fasahohin Sin.
Direktan cibiyar yin bincike kan manufofin raya kasa na kasar Senegal Ari Sow ya yi tsammani cewa, kasar Sin ta kafa tsarin bunkasuwa mai alamar Sin irin na gurguzu, kuma ta ci gaba da kyautata shi, kuma ta zama abin koyi ga kasashe masu tasowa.
Ministan kula da harkokin kasar Togo kuma kakakin gwamnati, Pascal A. Bodjona ya bayyana cewa, kasar Sin ta ba da misali ga kasashen Afirka kan yadda za a samu cigaba.(Zainab)
|