Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-01 21:04:22    
Sin ta samu karfi sosai sakamakon manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, in ji masanan Afirka ta kudu

cri

Kwanan baya, yayin da wasu masana biyu kan harkokin kasar Sin a jami'ar Stellenbosch da ke kasar Afirka ta kudu suke hira da manema labarai na kasar Sin, sun nuna babban yabo ga sauye-sauyen da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashe waje ta kawo wa kasar Sin. A ganinsu, Sin ta samu babban karfi daidai a sakamakon manufar.

Arnold Van Zyl, mataimakin shugaban jami'ar Stellenbosch, wanda ya taba zuwa kasar Sin har sau 20, ya ce, babu shakka, ba wata kasar da ta fi kasar Sin burge duniya a cikin shekaru 30 da suka wuce, kuma kasashen duniya sun ji irin manyan sauye-sauyen da suka auku ta fannonin tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a a kasar Sin. Ya yi nuni da cewa, sabo da karuwar karfin kasa, matsayin kasar Sin a duniya ya inganta. Tun lokacin da ta shiga kungiyar WTO a shekarar 2001, Sin na kara taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya. Yanzu "Sin ba ta iya rabuwa da duniya, haka kuma duniya na kara bukatar kasar Sin" ya riga ya zama ra'ayi daya na jama'ar duniya.(Lubabatu)