A ran 23 ga wata a Lima babban birnin kasar Peru, an kawo karshen kwarya kwaryar taron shugabannin kasashen kungiyar APEC a karo na 16. Bayan da aka bayar da sanarwar Lima ta game da tattalin arzikin duniya.
Sanarwar Lima dake da lakabin taken taron na sabon alkawarin bunkasa tattailin arzikin kasashen Asiya da na yankin tekun Pacific ta yi nuni da cewa, matsalar kudi da duniya ke fama da ita a yanzu matsalar ce mafi tsamari da kasashen kungiyar APEC ke fuskanta. A game da wannan batu, an bayar da sanarwa ta musamman, wannan ya bayyana niyyar kasashen kungiyar ta tinkarar yanayin duniya na tattalin arziki da yake tsamari da goyon bayansu na farfado da tattaunawar Doha tun da wuri da samun ci gaba.
Sanarwar Lima da shugabannin kasashen kungiyar APEC suka bayar a game da tattalin arzikin duniya ta yi nuni da cewa, dukkan mambobin kasashen kungiyar za su dauki karin matakai da daidaita ayyukansu a duk fannoni domin matsalar kudi. Kuma shugabannin kasashen kungiyar sun dau alkawari cewa, a watanni 12 masu zuwa, ba za su sanya sabbin shingayen ciniki ba wajen zuba jari, kayayyaki da himma. Bugu da kari, ba za su aiwatar da sabbin matakan kayyade yawan kayayyakin fici da shigi ba. Dadin dadawa, a dukkan fannoni, ba za su dauki matakan sabawa ka'idojin kungiyar ciniki ta duniya dake kunshe da matakin sa kaimi kan fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.
A cikin sanarwa, an yi bayanai kan daidaiton da mambobin kungiyar suka cimmawa a kan batun ingancin abinci, da samun isashen makamashi, da hadin kan tattalin arzikin yankuna, da nauyin dake wuyan kamfanoni kan zaman al'umma, da dumamar yanayi, da yaki da bala'i da dai sauransu.
An yi taron APEC a mataki na biyu a wannan karo a ran nan a Lima. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarci taron, kuma ya yi jawabi kan ciyar da tattalin arzikin yankuna gaba bisa tsarin bai daya, tsaron dan Adam, sauyawar yanayi da sauransu.(Asabe)
|