Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-13 21:16:15    
Kasashen Afrika suna fatan kara taka rawa wajen tinkarar matsalar kudi na duniya

cri
A kwanakin nan, shugaban kwamitin kungiyar AU Mr. Jean Ping ya ba da shawara cewa, ya kamata taron koli kan harkokin kudi da za a shirya a birnin Washington ya kara yi la'akari kan rawar da kasashen Afrika suka taka wajen tinkarar matsalar kudin duniya, ya kamata ya kara yin la'akari kan ra'ayin kasashen Afrika lokacin da aka tattauna batun kasuwar kudin duniya.

Bisa labarin da jaridar "Daily Nation" ta kasar Kenya ta bayar a ran 13 ga wata, an ce, a ganin Mr. Jean Ping, a cikin kasashen Afrika, kasar Afrika ta kudu ce kawai za ta iya shiga taron koli na kasashen 20 kan harkokin kudi da za a shirya a birnin Washington a ran 15 ga wata, wannan ba ya iya bayyana moriyar kasashen Afrika da amfaninsu ba.

A ran 15 ga wata, za a shirya taron koli kan harkokin kudi a tsakanin manyan kasashe 20 da suka hada da kasashe masu sukuni da na masu tasowa a birnin Washington, taron zai tattauna kasuwar kudi da batun tattalin arzikin duniya. (Zubairu)