Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-13 11:05:12    
Sun Zhenyu ya yi kira ga membobin kungiyar WTO da su dauki manufofin cinikayya masu yakini don warware rikicin hada-hadar kudi

cri
A ran 12 ga wata, a kwarya-kwaryan taron cinikayya na hukumar ciniki ta duniya WTO da aka yi a birnin Geneva, Sun Zhenyu, jakadan Sin da ke WTO ya bayar da wani jawabi, inda ya yi kira ga membobin WTO da su yi watsi da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, kuma su dauki manufofin cinikayya masu yakini don warware rikicin hada-hadar kudi na duniya ta hanyar sa kaimi ga cinikayya da habaka bukatu cikin gida.

Sun Zhenyu ya ce, rikicin hada-hadar kudi ya rage cinikayyar duniya. Bisa kiddidigar da asusun bada lamuni na duniya IMF ya bayar, yawan cinikayya na duniya a shekarar bana da ta badi zai ragu da kashi 5%, kuma membobin WTO, musamman masana'antu kanana da matsakaita na kasashe masu tasowa sun fuskanci matsaloli wajen samun rancen kudi da karuwar kudin da aka kashe don samun rancen kudi da fitar da kayayyaki.

Sun Zhenyu ya bayyana cewa, kasar Sin ta gabatar da manufofi goma don habaka bukatu cikin gida a makon jiya, kuma za ta kara zuba jarin da yawansu ya kai dala biliyan 580 kafin shekarar 2010, wadanda za su inganta karfin Sin wajen warware rikicin.(Zainab)