Shugabannin kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai wato EU sun kira wani kwarya kwaryar taro a ran 7 ga wata a birnin Brussels, bayan taron, shugaban kasar Faransa wadda ke rike da shugabancin EU a wannan karo Mr. Nicolas Sarkozy ya sanar da cewa, kungiyar EU za ta gabatar da shawarce shawarce wajen yin gyare gyare kan tsarin kudi na duniya na yanzu, da kuma matakai da za a dauka wajen tinkarar rikicin kudi a gun taron koli na kudi da za a shirya a birnin Washington a nan gaba ba da dadewa ba.
Hadaddiyar sanarwa da aka bayar bayan taron ta ce, kamata ya yi taron koli na duniya kan harkokin kudi da za a shirya a birnin Washington a ran 15 ga wannan wata zai aza wani harsashi wajen yin gyare gyare kan tsarin kudi na duniya. Shawarce shawarce da EU za ta gabatar za su hada da fannoni uku, wato na farko, ya kamata bangarori daban daban su samu ka'ida daya wajen kafa wani sabon tsarin kudi na duniya. Na biyu, ya kamata kasashe mahalartan taron su kaddamar da wani tsari, wanda yake iya yin amfani da shawarce shawarce na hakika. Na uku, kamata ya yi taron koli ya fitar da wani shiri domin tinkarar rikicin kudi a fannoni daban daban.(Danladi)
|