Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-08 17:13:11    
Shugabanni na kasashen da ke yammacin Afrika guda uku sun yi kira da kara yin tattaunawa kan rikicin shiyya-shiyya

cri
A ranar 7 ga wata a birnin Abidjan, babban birnin tattalin arziki na kasar Kodivwa, Mr. Laurent Gbagbo, shugaban kasar ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Benin Thomas Yayi Boni, da na kasar Togo Faure Gnassingbe, wadanda ke yin ziyara a kasar Kodivwa, inda shugabannin kasashen uku suka yi kira da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa ta hanyar tattaunawa a yankin rikici da ke Afrika.

A cikin haddadiyar sanarwar da aka bayar bayan shawarwarin, gaba daya shugabannin kasashen uku suna ganin cewa, ba za a tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a babban yankin Afrika ba a sakamakon rashin zaman lafiya da zama mai dorewa. Shugabannin kasashen uku suna damuwa kan tashe-tashen hankula da ake samu a kasashen Kongo Kinshasa, da Somaliya, da dai sauransu, kuma sun yi kira ga bangarori daban daban da ke cikin rikici da su yi shawarwari maimakon tayar da hargitsin nuna karfin tuwo.

Bugu da kari kuma, shugabannin kasashen uku suna kulawa da matsalolin da dukkan duniya ke fuskanta wajen abinci, da makamashi, da kuma kudi, bayan haka kuma sun maraba da kasashe daban daban da su dauki matakai don magance wadannan matsaloli. Kazalika kuma, shugabannin kasashen uku suna mayar da hankali kan taron koli game da sha'anin kudi na kungiyar kasashe 20 da za a shirya a ranar 15 ga wata a birnin Washington, suna fata za a kara ikon ba da jawabi na kasashen Afrika cikin tsarin kudi na duniya. (Bilkisu)