Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 15:39:37    
Makomar tattalin arzikin kasashen kungiyar EU ta shiga halin rashin tabbas, don haka sun dauki matakai don sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki

cri
Bisa rahoton kiyasta tattalin arziki a lokacin kaka da kwamitin kungiyar EU ya gabatar a ran 3 ga wata, an ce, tattalin arziki na kasashe 15 na yankin da ake amfani da kudin Turai da na kasashe 27 na kungiyar EU ya ragu a shekarar bana. Hakazalika kuma kasashe da yawa sun gabatar da matakai daban daban don warware rikicin hada-hadar kudi.

Rahoton kwamitin kungiyar EU ya kiyasta cewa, tattalin arziki na yankin da ke amfani da kudin Turai da na kasashe 27 na kungiyar EU za su ragu kashi 0.1% a karshen shekarar bana, kuma saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu a shekarar badi zai kai kashi 0.1% da 0.2%, tattalin arzikin yankuna zai ragu. Wani jami'in kula da harkokin tattalin arziki da kudadde na kwamitin kungiyar EU ya nuna cewa, a cikin membobin kasashen kungiyar EU, rikicin hada-hadar kudi ya kara tsanantar tabarbarewar tattalin arziki daga manyan fannoni.

Ban da wannan, wasu kasashe sun ci gaba da gabatar da matakai don warware rikicin hada-hadar kudi. Babban bankin Ingila zai yi taron da aka saba yi a kan manufofin kudadde a ran 6 ga wata, kuma bangarori daban daban suna fatan taron zai rage kudin ruwa daga kashi 0.5% zuwa kashi 4%. Gwamnatin Portugal za ta ba da shawara ga majalisar dokoki don mai da bankin ciniki na Portugal hannun 'yan kasa, wannan karo na farko ne da kasar Portugal ta mai da bankin ciniki hannun 'yan kasa tun daga shekarar 1975. Ma'aikatar kudadde ta kasar Koriya ta kudu ta gabatar a ran 3 ga wata cewa, za a kara kudin Koriya ta kudu da Yuan biliyan dubu 11 wajen kasafin kudin da za a kashe a shekarar 2009 don inganta manyan ayyuka da sa kaimi da zuba jari ga zamantakewar al'umma, kuma za a gudanar da matakan rage haraji da yawansu ya kai kudin Koriya ta kudu Yuan biliyan dubu 3.(Zainab)