Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-17 10:56:24    
Kasar Massar ta nuna cewar matsalar kudi ta duniya za ta kawo illa ga kasashen Afirka

cri

A ran 16 ga wata, minista harkokin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa na kasar Massar madam Fayza Mohamed Abu Naga ta yi gargadin cewa, matsalar kudi ta duniya za ta kawo illa ga kasashen Afirka a fannonin raya kasa da bunkasuwar tattalin arziki.

A gun taro kan rahoton tattalin arzikin Afirka na shekarar 2007 zuwa shekarar 2008 da bankin bunkasuwar kasashen Afirka ya shirya a ran nan, madam Fayza mohamed Abu Naga ta bayyana cewa, cikin shekarar 2007 a nahiyar Afirka yawan karuwar tattalin arziki ya kai kashi 6 bisa dari, kuma kasashen waje sun kara zuba jari ga sana'o'in raya ababen more rayuwar jama'a da sadarwa da aikin noma da masana'antu da yawon shakatawa da sauransu, amma nahiyar Afirka tana fuskatar kalubale wajen tabbatar da shirin burin bunkasuwan a sabon karni, musamman ma a bututuwan samar da hatsi da makamashi da kau da talauci da rashin daidaito a wajen samun albashi da rashin aikin yi da sauransu.

Madam Fayza Mohamed Abu Naga ta nanata cewa, dole ne kasashen Afirka su kara hadin gwiwa, kuma su fuskatanci kalubale na gaba tare. Ta yi kira ga kasashen Afirka da su tabbatar da gudanar da harkokin tattalin arziki ta hanyoyi daban-daban, da mai da hankalinsu a kan horaswa. A sa'I daya, ta yi kira ga kasashen masu wadata da su ba da taimako ga kasashen Afirka, don tabbatar da ganin bunkasuwar da kasashen Afirka suka samu a cikin wasu shekaru da suka wuce ba ta ja baya ba.(Abubakar)