Jiya 12 ga watan, shugabannin kasashen Turai 15 masu amfani da kudin Euro sun amince da wani shirin bai daya wajen shawo kan matsalar kudaden da suka fuskanta yanzu, inda suka amince da cewa gwamnatocin kasashensu za su sake ba da lamuni ga bankunansu, su ma za su ci gaba da saka jari a bankuna, don magance matsalar tattalin arziki da ke addabar duniya yanzu.
Bisa wata sanarwar da aka bayar a gun taron, an ce, mambobin kasashen Turai masu amfani da kudin Euro za su bayar da garanti ga sababbin basusuka na kasa da shekaru 5 da bankunan kasashensu suka bi kafin karshen shekarar 2009, kuma za su ci gaba da saka jari kai tsaye, don warware matsalar rashin samun kudade a sakamakon rikicin ba da rancen kudi a duniya yanzu.
A gun taron manema labaru, Nicolas Sarkozy, shugaban kasar Faransa wanda ke shugabancin kungiyar EU na wannan zagaye, ya bayyana cewa, shugabannin kasashen Turai sun yi alkawari cewa, ba za su amince da ko wace hukumar hada-hadar kudi ta yi durkushewa a cikin wannan rikicin kudi na duniya ba.(Bako)
|