Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-27 20:19:14    
Gamayyar kasa da kasa ta nuna yabo sosai kan nasarar da Sin ta samu wajen harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane

cri
A ranar 25 ga wata, kasar Sin ta samu nasarar harbar kumbo kirar ' Shenzhou-7' mai dauke da mutane, daya bayan daya wasu kusoshin siyasa, da mutane daga fannin kimiyya da fasaha sun nuna yabo sosai kan wannan, suna ganin cewa, wannan muhimmiyar ishara ce daban ga kasar Sin wajen tafiyar kumbon da ke dauke da 'yan sama jannati.

A ranar 26 ga wata, a lokacin da babban sakataren M.D.D. Ban Ki-Moon ke ganawa da jakada Zhang Yesui, sabon wakilin din din din na kasar Sin da ke M.D.D., ya taya murna sosai ga nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane da kasar Sin ta samu.

Bayan haka kuma, shugaban tarrayar majalisar jama'a ta kasar Switzerland Andre Bugnon, da shugaban hukumar zirga-zirgar sararin samaniya Yuriy Alekseyev, da dai sauransu su ma sun nuna yabo sosai kan wannan. (Bilkisu)