Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-27 16:56:05    
Kasar Sin za ta ba da gudummowa wajen yin amfani da sararin samaniya cikin lumana

cri
A ran 25 ga watan, an ci nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane na kasar Sin, mutanen kasar Sin dake kasashen waje sun taya murna a kan wannan, kuna suna ganin cewa, kasar Sin za ta ba da gudummowa wajen yin amfani da bincike sararin samaniya cikin lumana.

Shugaban kungiyar ciniki da masana'antu ta ksar Sin dake kasar Nijeriya Qian Guolin ya bayyana cewa, shi da abokansa sun kalli shirye-shiryen harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane. Ya ce, bayan an ci nasarar yin gasar wasannin Olympic ta Beijing, kasar Sin ta samu nasarar harbar kumbo mai dauke da mutane. Wannan zai yi amfani da dage matsayin kasar Sin a kasashen duniya.

A cikin kwanakin da suka wuce, mutanen kasar Sin dake kasar Afrika ta kudu sun mai da hankali a kan labarin harbar kumbo mai dauke da mutane.Mataimakin shugaban kungiyar hadin kan masana 'antu da cniki ta Shanghai dake Afrika ta kudu Si Hai ya bayyana cewa, ya yi ciniki a kasar Afrika ta kudu cikin shekaru da yawa, ya ga matsayin kasar Sin a kasashen duniya ya dage. Nasarar harbar kumbo mai dauke da mutane da aka samu tana bayyana cewa, fasahar kasar Sin a fannin sararin samaniya ta bunkasa.

Mai jagorar mutanen kasar Sin dake kasar Amirka Huang Keqiang ya bayyana cewa, nasarar harba kumbo mai dauke da mutane da aka samu ta bayyana cewa, kasar Sin ta iya ba da gudummowa a kan bncike da yin amfani da sararin samaniya.

A kan shafin tattaunawar Internet E ta arewacin kasar Amirka, ana mai da hankali sosai a kan harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane.

Shugaban kungiyar mutanen kasar Sin dake kasar Mongolia Bai Shuangzhan da kungiyar hadin kan mutanen kasar Sin dake kasar Mexico sun bayyana cewa, nasarar harba kumbo mai dauke da mutane da aka samu ta nuna cewa, fasahar sararin samaniya ta kasar Sin ta bunkasa da yawa. Kuma bunkasuwar fasahar kasar Sin za ta ba da gudummowa ga sana'ar sararin samaniya ta duniya. (Asabe)