A ran 25 ga wata a cibiyar harba tauraron dan Adam mai suna Jiuquan, an samu nasarar harba kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane, kafofin watsa labaru na kasashe daban daban sun nuna babban yabo ga lamarin bi da bi, suna ganin cewa, wannan ya zama sabon cigaba a sha'annin harba kumbo mai dauke da mutane kuma ya kara wa jama'ar kasar Sin alfahari.
Jaridar kasuwanci ta Nanyang ta Malaysia da Jaridar Mainichi Shimbun ta Japan da jaridar Le Figaro ta Faransa da kuma jaridar Washington Post ta kasar Amurka sun bayar da rahotanni kan kumbo kirar "Shenzhou-7", sun ce, harba kumbo kirar "Shenzhou-7" dauke da mutane cikin nasara ya nuna cewa, fasahar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin ta samu babban cigaba.
Hakazalika, kafofin watsa labaru na kasashen Portugal da Nicaragua da Honburas da kuma sauransu sun ba da labaru masu kyau ga wannan lamari.(Lami)
|