Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 16:34:17    
Mutanen Sin da ke a kasashen waje sun taya murnar samun nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane

cri
A ran 25 ga wata, an samu nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane na kasar Sin, mutanen Sin da ke a kasashen waje bi da bi ne sun taya murna ga wannan.

Kungiyar sa kaimi ga dinkuwar duk kasar Sin da ke a kasar Ingila ta bayyana cewa, dukan mutanen Sin da ke a kasashen waje sun ji dadi sosai a kan samun nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7", kuma wannan abin al'ajabi ne da al'ummar Sin ta girgiza duniya bayan da ta samu nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Dr Chen Anshen, mataimakin shugaban kungiyar mutanen Sin da ke a Austria ya ji farin ciki sosai a kan saurin bunkasuwar kimiyya da fasaha na kasar Sin. Yana da imani cewa, bunkasuwar kimiyya da fasaha na kasar Sin za ta sa kaimi ga bunkasuwar aikin kawo albarka, kuma za ta inganta tattalin arzikin Sin zuwa wani sabon mataki.

Huang Sunxiang, shugaban kungiyar 'yan abokan karatu ta jami'ar kimiyya da fasaha ta kasar Sin da ke a yankin Washington na Amurka ya ce, daliban da ke karatu a kasar Amurka sun ji farin ciki da alfarma a kan cin nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7". Wang Zhonglin, masana mai bincike fasahar nanometer na kwarijin kimiyya na Georgia na kasar Amurka ya bayyana cewa, aikin harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" ya bayyana bunkasuwar karfin kimiyya da fasaha ta kasar Sin, kuma wannan shi ne babban cigaba da mutanen Sin ke samu wajen bincike sararin samaniya.(Zainab)