 A ran 17 ga wata, an samu fashewar boma-bomai da aka dasa a cikin mota kusa da ofishin jakadancin kasar Amurka a birnin San'a, hedkwatar kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 16 a kalla. Kwamitin sulhu na MDD da kasar Amurka sun yi Allah wadai da wannan dauyen ciki.
Wani jami'in Yemen ya tabbatar da cewa, an kai harin boma bomai da aka dasa a cikin mota kusa da ofishin jakadancin Amurka a Yemen a wannan rana. An yi musanyar wuta tsakanin 'yan bindiga da rundunar sojan tsaro ta Yemen. Ya zuwa yanzu a kalla mutane 16 suka mutu sakamakon lamarin, a cikinsu da akwai 'yan bindiga 6, da sojojin Yemen 6, da farar hula 4.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, wata kungiya mai dauke da makamai da ake kiran kanta kungiyar Jihadi ta musulunci ta Yemen ta sanar da daukar nauyi na wannan farmakin boma bomai, kuma ta yi shelar cewa za ta kai irin wannan farmaki ga afisoshin jakadanci na Ingila da na Saudi Arabia da na hadaddiyar daular Larabawa a Yemen.
Kakakin kwamitin tsaron kasa na kasar Amurka Mr. Gordon Johndroe ya bayyana cewa, kasar Amurka ta yi Allah wadai da farmakin da aka kai wa ofishin jakadancinta dake kasar Yemen, batun nan ya nuna shaida cewa, har wa yau dai, kasar Amurka tana fuskantar barazanar ta'adanci a kasashen waje. Kasar Amurka za ta ci gaba da hadin gwiwa da gwamnatin kasar Yemen a kan aikin yaki da ta'adanci, don rigakafin sake aukuwar irin wannan lamari. (Zubairu)
|