Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 21:57:25    
Wasu shugabannin kasashen waje sun taya murnar shirya wasannin Olympics na Beijing cikin nasara

cri
A 'yan kwanakin nan da suka gabata, wasu shugabannin kasashe da na kungiyoyin duniya sun mika sakwanni da wasiku ga kasar Sin don taya murnar shirya wasannin Olympics na Beijing cikin nasara sosai.

Shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing wani gagarumin biki ne na duk duniya wanda ya ba mu mamaki sosai, kuma ta hanyar shirya gasar, an nuna wata sabuwar kasar Sin da ta samu manyan nasarori a idon duk duniya. Ya yi imanin cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta zama tamkar wata ishara ce a tarihi.

Firayim ministan kasar Kuwait Nasser Al-Sabah kuma ya bayyana cewa, ayyukan shirya wasannin Olympics na Beijing na da kyau kwarai da gaske, wadanda suka samar da kyawawan sharuda da muhalli mai adalci ga 'yan wasa wajen nuna gwaninta.

Haka kuma babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing ta ba da mamaki sosai, ya kamata kasar Sin ta yi alfahari da ita. Wannan gagarumin biki ya sa 'yan wasa da jama'a da kuma shugabannin kasa da kasa sun taru don taya murnar ruhin Olympics, kuma wannan ita ce babbar gudummowa da kasar Sin ta samar don raya wata kyakkyawar duniya.(Kande Gao)