Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-27 20:32:23    
Gasar wasannin Olympics ta Beijing ta sanya duniya ta fahimci kasar Sin

cri
A ranar 26 ga wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun cigaba da bayar da labarai kan gasar wasannin Olympics ta Beijing, ana ganin cewa, gagarumar gasar wasannin Olympics ta kara kusantar da kasar Sin ga duniya, a waje daya kuma ta sanya duniya ta fahimci kasar Sin.

Jaridar The Sun ta hukumar kasar Senegal, da jaridar Daily ta kasar, da kuma sauran jaridu sun bayar da labarai da hotuna, inda suka nuna yabo sosai ga gasar wasannin Olympics ta Beijing, sun ce wannan gasar mai kyau kuma mai ban mamaki, a waje daya kuma sun nuna cewa, 'yan wasa na Afrika sun samu sakamako mai kyau ne a sakamakon ayyukan shirye-shirye masu kyau.

A ran 26 ga wata, jaridar "Les Depeches De Brazzaville" ta kasar Kongo Brazzaville ta bayar da bayanin edita cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta zama gasar wasannin Olympic mafi kyau, da girma, da kuma kyakkyawan shiri, shi ya sa, ta zama gasa mafi kyau wajen shaida wa mutane karfin kasa. Ta gasar wasannin Olympic ta Beijing, mutane sun canja ra'ayoyinsu game da kasar Sin, mutanen kasashen waje sun kara fahimtar ainihin hali da kasar Sin ke ciki.

Bugu da kari kuma, kafofin watsa labaru na kasashen Kodiva, da Uganda, da Amurka, da Faransa, da dai sauansu, su ma sun bayar da labarai son waiwayi gasar wasannin Olympics, kuma sun nuna yabo sosai ga ayyukan share fage na gasar. (Bilkisu)