Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-26 16:33:34    
Mutanen kasar Sin da daliban kasar Sin dake kasashen waje sun yi bukukuwa don taya murnar rufe wasannin Olympic na Beijing

cri

A ran 24 ga wata da dare a birnin Beijing, an rufe wasannin Olympic na yanayin zafi a karo na 29. Mutanen kasar Sin da daliban kasar Sin dake kasashen waje sun yi bukukuwa don taya murnar rufe wasannin Olympic na Beijing.

A ran nan, kungiyar mutanen kasar Sin da mutanen lardin Fujian suka kafa a kasar Amirka sun yi bukukuwa bi da bi a birnin New York. Mutanen kasar Sin dake kasar Amirka sun sha bayyana cewa, a karo na farko ne kasar Sin ta samu lambobin zinariya mafi yawa a wasannin Olympic, duk jama'ar kasar Sin suna farin ciki sosai da yin alfahari a kan wannan.

Wasu daliban kasar Sin dake kasar Japan sun yi taro da kallon bikin rufe wasannin Olympic na Beijing a sashen ba da ilmi na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Japan. Wani wakilin daliban kasar Sin dake kasar Japan ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi wasannin Olympic na Beijing cikin nasara ba kawai kan gasanni ba, hatta ma ta ci nasara a kan tattalin arziki da wayewar kan kasar.

A birnin Johannesburg, mutanen kasar Sin dake kasar Afrika ta kudu da yawa sun taru, kuma sun kalli bikin rufe wasannin Olympic na Beijing. Sun bayyana cewa, babbar nasara da aka ci a kan wasannin Olympic da sakamako mai kyau da 'yan wasan kasar Sin suka samu sun nuna cewa, kasar Sin tana yi ta bunkasuwa.(Asabe)