Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-26 11:57:57    
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yabawa gasar wasannin Olympic ta Beijing cewa tana da ma'anar musamman sosai

cri

Bayan an rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, kafofin watsa labaru na kasashen waje sun bayar da labarai da dama a ran 24 da 25 ga wata, inda suka yaba wa aikin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing sosai, cewa kyakkyawar wasan kwaikwayo da aka yi a bikin bude da rufe gasar wasannin Olympic, da sakamakon gasannin da aka samu sun nuna mana karfin kasar Sin, suna da ma'anar musamman sosai.

A ran 25 ga wata, shahararrun jaridu guda 5 na kasar Birtaniya sun bayar da labarai da hotuna game da rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing. Jaridar "The Independent" ta bayar da labarin cewa, tsarin gasar wasannin Olympic ta Beijing kasaitaccene, kuma babu aibu a cikin aikin shirya gasar, har yanzu, ta zama gasar wasannin Olympic mafi kyau da aka taba gani.

A ran 25 ga wata kuma, kafofin yada labaru na kasar Faransa sun bayyana cewa, kasar Sin ta shaida wa mutane iyawarta ta hanyar shirya gasar wasannin Olympic. Kafofin watsa labaru na kasar Afrika ta kudu sun bayyana cewa, ba a taba ganin irin wadannan abubuwa masu burgensa ba da gasar wasannin Olympic ta Beijing ta nuna.

A ran 25 ga wata, kamfanin dillacin labaru na kasar Iran, wato IRNA, ya bayar da bayanin edita cewa, gasar wasannin Olympic ta shaida wa mutane sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin bunkasuwar tattalin arziki, da na zama rayuwa a cikin shekaru kusan 30 da suka wuce, kuma ta shaida wa mutane karfin kasar Sin.

Manyan jaridun kasar Australia kamar jaridar "The Australian" sun bayar da labarai a ran 25 ga wata cewa, yanzu, ba za a iya musunta karfin kasar Sin a fannin siyasa, da tattalin arziki, da al'adu.

A ran 24 kuma, jaridar "Los Angeles Times" ta kasar Amurka ta bayar da labari cewa, babu aibi a aikin shirya gasar wasannin Olympic nan, ya zama wata nasara da jama'ar kasar Sin suka samu wajen shaida wa duk duniya karfinsu. Jaridar "Washington Post" ta bayar da labari cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta bayyana karfin kasar Sin wajen tattalin arziki da kimiyya da fasaha a matsayin wata babbar kasa.

Sauran manyan kafofin watsa labaru na kasashen New Zealand, da Malta, da Romania, da Czech, da Mexico, da Bangladesh, da Algeria, da Kenya, da Honduras, da Singapore, da Cambodia, da kuma sauran kasashe sun yabawa aikin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing bi da bi, cewar ta zama wani babban bikin ne a tarihi. (Zubairu)