Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-26 10:56:13    
Wasu shugabannin kasashen Afirka sun aika da sako domin taya murna ga nasarar da kasar Sin ta samu wajen gudanar da wasannin Olympic

cri

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wasu shugabannin kasashen Afirka sun aika wa shugaba Hu Jintao na kasar Sin da firayin minista Wen Jiabao da mataimakin shugaba Xi Jinping sako domin taya murna ga kasar Sin da ta samu nasarar gudanar da gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma sun yaba wa gudummowar da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suka bayar ga wannan lamari.

Shugaba Bingu Wa Mutharika na kasar Malawi ya bayyana cewa, a cikin dogon lokaci kasar Sin ta ba da gudummowa sosai wajen ciyar da zaman lafiya na kasashen duniya gaba da kara fahimta tsakanin jama'ar kasashen duniya. Jama'ar kasar Malawi suna farin ciki kwarai bisa ga yadda jama'ar kasar Sin suka cimma nasarar gudanar da gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Shugaba Pedro Verona Rodrigues na kasar Cape Verde ya bayyana cewa, taken wasannin Olympic na 'duniya daya buri daya' da kasar Sin ta bayar ya kasance abin koyi wajen ingiza hadin kai da zumunta tsakanin jama'ar kasa da kasa.

Shugaba James Alix Michel na kasar Seychelles ya bayyana cewa, kasar Sin ta cimma nasara wajen yaki da bala'in girgizar kasa mai tsanani, kuma ta cimma nasarar gudanar da wasannin Olympic na Beijing. Ta shaida tunanin hakuri da iyawar magance duk wahaloli da kalubale na jama'ar kasar Sin ga duk duniya. Tunanin 'tsabtataccen Olympic da Olympic na kimiyya da fasaha da Olympic na al'adun dan adam' da gasar wasannin Olympic ta Beijing ta bayar ya dace da tunanin bunkasuwa na jama'ar kasar Seychelles sosai.

Shugaba Ernest Bai Koroma na kasar Sierra Leone yana fatan alheri da kasar Sin za ta samu nasarar gudanar da gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu.

Shugaba Omar Hassan Al-Bashir na kasar Sudan ya bayyana cewa, an yi aikin hidima a duk fannoni a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma an samar da kyawawan shirye shirye a gun bikin bude gasar. Lalle gasar wasannin Olympic ta Beijing ta zama gasar wasannin Olympic bisa babban matsayi mai alama a cikin tarihi.

Shugaba Abdelaziz Bouteflika na kasar Algeria ya nuna babban yabo ga ayyukan shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, kuma ya yi imani cewa, dangantakar hadin kai tsakanin kasashen Sin da Algeria za ta bunkusa cikin dogon lokaci.(Fatima)