A ran 24 ga wata da dare, Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya ya bayar da wata sanarwa, inda ya taya murna ga 'yan wasan kasar da suka samu lambobin zinariya 5 da na azurfa 5 da na tagulla 4 a cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing, wanda ya zama maki mafi kyau tun bayan shekarar 1956 da kasar Kenya ta fara shiga gasar wasannin Olympics.
A cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing, 'yan wasan Kenya sun samu nasarori, a jere kuma sun samu lambar zinariya ta mata ta farko kuma da lambar zinariya ta gasar Marathon ta farko a tarihi, yawan lambobin wasannin Olympics da kasar Kenya ta samu ya fi yawa a tarihi, kuma ya zama matsayi na 15 a jerin sunayen kasashen da suka samu lambobin ziniriya a gasar, wanda ya zama matsayi na farko a cikin dukan kasashen Afirka masu halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing.
Mr Kibaki ya ce, jama'ar kasar Kenya suna alfarma sosai a kan sakamakon mai kyau da 'yan wasan kasar suka samu, kuma sun samu yabo daga dukan nahiyar Afirka. Mr Kibaki ya sanar da cewa, za a yi bikin taya murnar dawowar 'yan wasan kasar a ran 29 ga wata.(Zainab)
|