Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 16:53:54    
Kamfannonin watsa labaru na kasa da kasa da jama'ar sun darajanta gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
A ran 24 ga wata da dare ne, aka rufe gasar wasannin Olympic a karo na 29 da aka shafe kwanaki 16 ana gudanarwa a birnin Beijing. Bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, da ainihin ruhu da yan wasannin Olympic suka nuna, da wasan kwaikwayo a bikin rufe gasar, dukkansu su shaida wa mutanen duniya wani babban bikin wasannin motsa jiki da ba a taba ganin irin sa ba. Kafofin watsa labaru na kasa da kasa da jama'ar sun yabawa gasar wasannin Olympic ta Beijing sosai, kuma sun taya murnar cimma nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Gidan telebijin na farko na kamfanin watsa labaru na kasar Kenya ya ba da shirin kai tsaye game da bikin rufe gasar a ran 24 ga wata. Lokacin da shugaban kwamitin wasannin Oylmpic na duniya Mr. Jacques Rogge ya ba lambar zinariya ga dan wasan kasar Kenya wanjiru kamau da ya sami lambawan ta gasar gudun dogon zango wato Marathon na maza, kuma an daga tutar kasar Kenya da rera wakar kasar Kenya, mai jagorancin shirin Mr. Milton Nyakundi ya bayyana cewa, a lokacin, bai iya sifanta zuciyarsa ba, mutanen duniya sun zura ido kan kasar Kenya. Mr. Milton ya yaba wa bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing cewa, bikin ya bayyana cewa, al'adun daban daban, na zamani da na da, na gida da kuma na waje, dukkansu su iya zaman tare cikin lumana, bikin ya kawo kyakkyawan karshe ga gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Gidan telebijin na Televisa na kasar Mexico shi ma ya bayar da shirin game da bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing kai tsaye. Mai jagorancin shirin ya bayyana cewa, birnin Beijing ya shirya wata gasar wasannin Olympic mafi kyau a tarihi, duk mutanen duniya sun kara fahimta game da bunkasuwar kasar Sin, da himmar da jama'ar Sin suke yi ta babban bikin wasannin motsa jiki nan.

A kasar Amurka, kamfanin watsa labaru na NBC ya dage lokacin da aka bayar da shirin game da bikin rufe gasar wasannin Oilympic da owoyi 12 don kara yawan mutane da suke iya kallon bikin, a cikin shirin, ya nuna hotuna da aka dauka lokacin da yan wasa na kasar Amurka suke cimma nasarar gasanni.

Kamfanin dillancin labaru na AP kuma ya bayar da labari cewa, birnin Beijing ya cimma burinsa na shirya wata gasar wasannin Olympic cikin nasara. Aikin ba da tabbaci ga gasar wasannin Olympic ta Beijing da aikin tsaro suna da kyau sosai.

Manyan kamfannonim yada labaru na kasashen Koriya ta kudu, da Tailand, da Singapore, da Rasha, da Jamus, da Austria, da dai sauransu su ma sun bayar da labarai, inda suka yabawa gasar wasannin Olympic ta Beijing sosai.

A gun bikin rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, birnin Beijing ya mika wa birnin London tutar wasannin Olympic, gasar wasannin Olympic ta shiga lokacin London. Kamfanonin watsa labaru na kasar Birtaniya sun bayar da labarai don taya murnar cimma nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, a sa'I daya kuma, sun ce birnin London zai yi koyi daga wajen birnin Beijing, don shirya maraba da gasar wasannin Olympic ta London. (Zubairu)