Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-25 16:17:30    
Bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing yana da kyau sosai

cri

A ran 24 ga wata, a birnin Dakar, bayan da Mamadou Koume, shugaban kamfanin dillancin labaru na Senegal ya dubi bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing ta hanyar TV kai-tsaye, ya bayyana cewa, bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Beijing ya kasance gagarumi kuma yana da kyaun gani, kuma ya burge jama'a, yana da kyau sosai tare da bikin bude gasar.

Mr Koume ya ce, bisa labarin da dan jarida musamman na kamfanin dillancin labaru na Senegal da ke a Beijing ya bayar, gasar wasannin Olympics ta Beijing ya kasance gagarumi kuma yana da kyaun gani, aikin share fage ya yi kyau, jama'ar Sin suna da son baki, gasar ta shaida nufin Olympics, kuma ta shaida bunkasuwar kasar Sin da jituwarta.

Ya ce, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na Senegal ya yi hasashe kafin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, kasar Sin ta rinjayi kasar Amurka wajen samun lambar zinariya, kuma ta samu yabawa daga dukkan kasashen duniya.

Mr Koume ya bayyana cewa, yana fatan kasashen Sin da Senegal za su aika masu koyawa da wasan motsa jiki ga juna don kara yin mu'ammala a fannin wasan motsa jiki.(Zainab)