|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-08-24 19:20:35
|
 |
Ya kamata a bayar da wata babbar lambar zinariya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing, a cewar kasashen duniya
cri
Bisa kusan karewar gasanni daban daban na wasannin Olympics na Beijing, a 'yan kwanakin da suka wuce, daya bayan daya kasashen duniya suka nuna yabo sosai ga wasannin, kuma suna ganin cewa, ya kamata gasar wasannin Olympics ta wannan karo, ita da kanta ta samu wata babbar lambar zinariya, ana iya kiranta 'Wasannin Olympics mai lambar zinariya'.
Shagdarjav Magvan, mamba mai girmamawa na hukumar wasannin Olympics ta duniya, ya ce, ko ayyukan share fage, ko ayyukan shirye-shirya a lokacin gasanni, wasannin Olympics na Beijing ya kai wani babban matsayi.
Shugaban birnin Berlin na kasar Jamus Klaus Wowereit ya ce, wasannin Olympics na Beijing zai ba da taimako kan bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin ke yi.
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Amurka Peter Ueberroth ya bayyana cewa, jama'ar kasar Sin sun shirya wani wasannin Olympics cikin nasara sosai,
Shugaban kungiyar wasannin motsa jiki ta kasar Masar Mohammed Kamal Shahin na ganin cewa, wasannin Olympics na Beijing da kyau sosai, ya wuce dukkan wasannin Olympics na da a fannonin manyan gine-gine, da dakuna da filayen motsa jiki, da kuma ayyukan shirya gasanni. A ganinsa, wannan wasannin Olympics zai zama wasannin Olympics da ya fi girma a tarihi. (Bilkisu)
|
|
|