Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-24 16:53:04    
Kafofin watsa labaru na Kenya sun yaba wa 'yan wasa na kasar domin maki mai kyau da suka samu a Beijing

cri
A gun gasannin guje-guje na wasannin Olympic na Beijing da aka yi a ran 23 ga wata, 'yan wasa na kasar Kenya sun samu lambobin zinariya 2 da wata lambar azurfa tare da lambar tagulla biyu. Sabo da haka, gidan talabijin da jaridu daban daban na kasar Kenya sun bayar da bayanai a wannan rana, inda suka yaba wa maki mai kyau da 'yan wasa na Kenya suka samu a Beijing.

A gun gasar karshe ta guje-guje ta maza ta mita 800 da aka yi a wannan rana da dare, Wilfred Bungei na Kenya ya samu wata lambar zinariya, abokin wasansa Alfred Kirwa Yego ya samu wata lambar tagulla. Sannan a gun gasar karshe ta guje-guje ta mata ta mita 1500, Nancy Langat ta samu wata lambar zinariya. Daga baya, a gun gasar karshe ta guje-guje ta maza ta mita 5000, 'yan wasa biyu na kasar Kenya sun samu wata lambar azurfa da wata lambar tagulla.

Tasha ta farko ta kamfanin rediyon kasar Kenya, wato KBC ta watsa wadannan gasanni uku kai tsaye. Bayan an kammala gasar, wanda ke jan akalar wannan shiri da masu ba da sharhi kan wasannin motsa jiki biyu sun ji farin ciki sosai sabo da makin da 'yan wasa na Kenya suka samu. Sun ce, kasar Kenya ta kafa abin al'ajabi. Ya kamata a rubuta wannan ran 23 ga watan Agusta a cikin takardun tarihi.

A waje daya kuma, jaridar "The Standard" ta Kenya ta bayar da wani bayani da ke da lakabi haka: "Kasar Kenya ta samu lambobin zinariya a cikin kwana daya", inda wakilinta da ke nan Beijing ya kai wa Bungei ziyara. Mr. Bungei ya ce, a da, bai taba tsammanin cewa zai iya shiga gasar wasannin Olympic, kuma zai iya samun lambar zinariya ba. Sabo da haka, yana farin ciki sosai domin samun wata lambar zinariya a birnin Beijing.

Bugu da kari kuma, a kan shafin internet na jaridar "Daily Nation" ta Kenya, ko da yake tarzomar da aka yi a farkon shekarar da muke ciki sakamakon babban zaben kasar ta yi mummunar tasiri sosai ga 'yan wasa, amma 'yan wasa na kasar Kenya sun yi kwazo da himma sun yi yaki da wahalolin da suka samu, kuma sun samu maki mai kyau sosai. (Sanusi Chen)