Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-20 21:46:41    
Shugaban kasar Nijeriya ya ba da kwarin gwiwa ga kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta kasar

cri

A ran 19 ga wata, bayan da kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta kasar Nijeriya ta lashe kungiyar kasar Belgium da hudu da daya a cikin karon kusan karshe na wasan kwallon kafa na Olympics na Beijing, nan da nan jama'ar kasar Nijeriya sun fara nuna farin ciki da jin dadi, har ma shugaba Umaru Musa Yar'Adua ya taya murna ga kungiyar 'yan wasa ta kasar.

Kakakin shugaba Yar'Adua ya ce, shugaba Yar'Adua yana jin dadi sosai, yana son wasan kwallon kafa, kuma yana mai da hankali sosai kan kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta kasar Nijeriya, yana fatan za ta samu lambar zinariya.

Mr. David Mark shugaban majalisar dattijai ta kasar Nijeriya ya yi imanin cewa, kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta kasar Nijeriya za ta sake samun lambar zinariya kamar nasarar da ta taba samu a cikin gasar wasan kwallon kafa ta wasannin Olympics ta Atlanta ta shekarar 1996.