![]( /mmsource/images/2008/08/17/m080817001.jpg)
Ran 16 ga wata da dare a filin wasa na Olympic na birnin Qinhuangdao, an yi gasar neman shiga cikin gasar semi-final ta wasan kwallon kafa maza ta wasannin Olympics na Beijing a tsakanin kungiyar kasar Nijeriya da kungiyar kasar Cote d'Ivoire, kasar Nijeriya ta lashe kasar Cote d'Ivoire biyu da ba ko daya, haka kuma ta shiga cikin gasar semi-final.
![]( /mmsource/images/2008/08/17/m080817002.jpg)
Yayin da ake yin wannan gasa, kide-kiden da abokanmu na kasar Afirka suke yi a wuri da ihun sa kaimi da 'yan kallo fiye da dubu 22 na kasar Sin suke yi sun yi musanya tare. A mintoci 44, 'dan wasa mai suna Odemwingie na kasar Nijeriya ya yi harbi mai dogon zango, kungiyar kasar Nijeriya ta ci gwal na farko.
![]( /mmsource/images/2008/08/17/m080817003.jpg)
A yayin da ke da sauran mintoci 9 kafin an gama gasa, kungiyar kasar Nijeriya ta sami damar buga Penalty. 'Dan wasa Obinna shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Nijeriya ya ci gwal na biyu.
A ran 19 ga wata da karfe 6 na yamma bisa agogon Beijing, wato karfe 11 na safe bisa agogon Nijeriya, za a yi gasar semi-final na wasan kwallon kafa a tsakanin kungiyar kasar Nijeriya da kungiyar kasar Belgium a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin.
|