Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-16 20:13:03    
Hugo Chavez ya yaba wa ayyukan shirye-shirye na wasannin Olympics na Beijing

cri
A ranar 15 ga wata a birnin Asuncion, babban birnin kasar Paraguy, shugaban  kasar Venezuela Hugo Chavez ya nuna yabo sosai ga ayyukan shirye-shirye na wasannin Olympics na Beijing, kuma ya ce, kullum yana kallon gasanni har a duk tsawon dare.

Mr. Chavez, wanda ke halartar bikin yin rantsuwar kama mukami na Fernando Lugo, sabon shugaban kasar Praguay, ya bayyana a gun wani taron manema labaru cewa, shirya wasannin Olympics na Beijing cikin nasara, wannan na nuna wa dukkan duniya wata kasar Sin da ta sha bambanci sosai bisa ta shekaru fiye da 50 da suka wuce, yanzu kasar Sin na zama wata babbar kasa da ke iya kawo tasiri sosai a karni 21. Ya ce, wannan ne wasannin Olympics da ya fi kyau a tarihi.

Bayan haka kuma, Mr. Chavez ya bayyana cewa, ba kawai kasar Sin ta nuna karfin iyawar shirye-shirye a gun wasannin Olympics na Beijing ba, har ma ta nuna cigaban da ta samu a fannin motsa jiki. (Bilkisu)