Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 14:46:00    
(Sabunta)Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yaba wa wasannin Olympic na Beijing sosai

cri
A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wasu manyan kafofin watsa labaru na kasashen waje sun ba da bayani kan kyakkyawan sakamakon lambar zinari da ta azurfa da 'yan wasa na kasar Sin suka samu a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing. A sa'i daya kuma sun yaba wa aikin shirya da hidima mai kyau da ake bayarwa a wasannin Olympic na Beijing

Jaridar Al-Ahram, wato wata muhimmiyar jarida ta kasar Masar ta ba da bayanin edita a jere a cikin 'yan kwanaki, inda ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta kunshi sakamakon bunkasuwa da kasar Sin ta samu a cikin lokacin bude kofar Sin ga kasashen waje. Bayanin edita ya bayyana cewa, taken 'Duniya Daya Mafarki Daya' ya zo daga tunanin Confucius na shekaru dubu na kasar Sin. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasar Sin ta gabatar da tunanin neman bunkasuwa mai jituwa, wanda shi ne sake fahimta ga tunanin Confucius da amfani da shi a cikin hakikanin halin a ake ciki. Tunanin neman jituwa ya shaida jimiri da kuzari da karfin cigaba.

Ran 14 ga wata, jaridar Daily Nation da aka fi bugawa a kasar Kenya ta ba da labari a shafin motsa jiki, kuma ta dauki misali da hidimar harsuna da aka yi a gun gasar wasannin Olympic domin nuna babban yabo cewa, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing yana ba da kyakkyawar hidimar harsuna ga mutanen kasashen waje da ke ziyara a Beijing, wanda ta faranta ran duk mutanen kasashen waje da ke cikin birnin Beijing.(Fatima)