Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-15 14:38:35    
Gidan jakadanci na kasar Sin da ke a kasar Kenya ya fadakar da gasar wasannin Olympics ta Beijing ga daliban kasar Kenya

cri
Karamar kungiyar rudunar 'yan mata ta gidan jakadanci na kasar Sin da ke a kasar Kenya ta gayyaci dalibai fiye da 70 na kwalejin bunkasuwar zamantakewa na Kenya a ran 14 ga wata, kuma ta shirya musu wake-wake da raye-raye na gargajiyar Sin da kuma fim na Sin don fadakar da al'adun kasar Sin da gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Cai Xiaoli, matar jakadan Sin da ke wakilci a Kenya ta ce, dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasar Sin da ta Kenya tana cikin hali mai kyau, kuma bangarori biyu suna fatan kara musanyar al'adunsu da juna. Yanzu ne ana yin gasar wasannin Olympics a Beijing, wannan lokacin samun dama ne na fadakar da kasar Sin gare su.

Joan Githae, shugabar kwalejin bunkasuwar zamantakewa na Kenya ta bayyana cewa, wannan shi ne kyakkyawan bikin musanyar al'adu, ta ga abubuwan kama da juna da ke tsakanin al'adun kasar Sin da na Kenya, alal misali bangarori biyu suna mai da hankali kan hadin gwiwa tsakanin jama'ar kasa.(Zainab)