Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-14 16:16:02    
Gasar wasannin Olympic na Beijing ta shaida cewa karfin kasar Sin yana kara karuwa

cri
A cikin kwanakin nan, kamfannin dillancin labaru na ketare suna mai da hankula sosai a kan gasar wasannin Olympic ta Beijing, sun yaba wa ra'ayin musamman na bikin bude gasar wasannin Olympic da aikin shirya da gwamnatin Sin da jama'ar ke yi, kuma suna zaton cewa, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shaida cewa, karfin kasar Sin yana ta kara karuwa.

A kwanakin baya, lokacin da manema labaru na jaridar "The Standard" ta kasar Kenya Mr. Omulo Okoth yake yi intabiyu game da gasar wasannin Olympic a birnin Beijing, ya yabawa gine-ginen cibiyar manema labaru na wasannin Olympic na Beijing, da kyakkyawar hidima da masu aikin sa kai suka gabata, ana jin dadi a ko ina.

Kamfanonin dillancin labaru na kasar Amurka sun siffanta halin da kasar Sin ta nuna ta hanyar shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. A ran 11 ga wata, jaridar "Washington Post" ta bayar da labari cewa, jama'ar kasar Sin sun nuna matukar sha'awa kan gasar wasannin Olympic. Mujallar "Time" ta bayyana cewa, wake-wake da raye-raye da aka yi a gun bikin budewa sun nuna wayin kai mai wadata a tarihin shekaru 5000 na kasar Sin ga mutanen duniya. Lokacin da aka kunna babbar wutar yola ta gasar wasannin Olympic, an shaida wa dukkan mutanen duniya abin gaskiya cewa, kasar Sin ta dawo tare da girmammawa. (Zubairu)