Ran 13 ga wata, bi da bi ne manyan kafofin watsa labaru na kasar Afirka ta kudu sun yabawa 'yan wasan kasar Sin saboda lambobin da suka samu a cikin gasannin Olypmic na Beijing.
A wannan rana, "jaridar Cape Town" ta kasar Afirta ta kudu ta rubuta a shafi na farko da cewa, "'Yan wasan kasar Sin sun girgiza duniya!"
A ran 13 ga wata, gidan TV na kamfannin rediyon kasar Afirka ta kudu ya yi sharhi kan kungiyar 'yan wasa mata ta kasar Sin wadda ta samu lambar zinariya ta gasar lankwashe jiki tsakanin kungiyar mata, ya ce, bayan kungiyar 'yan wasa maza ta kasar Sin ta samu lambar zinariya ta gasar lankwashe jiki tsakanin kungiyar maza a ran 12 ga wata, kungiyar 'yan wasa mata ta kasar Sin ta kafa wannan kyakkyawan sakamako a tarihi.
A ran 13 ga wata, Mr. Steven Matale mai da ba sharho kan wasan motsa jiki ya bayar da sharhi kan jaridar "Pretoria News" cewa, 'yan wasan kasar Sin sun samu kyakkyawan sakamako cikin gasannin harbe-harbe, da daga nauyi, da tsinduma cikin ruwa, da lankwashe jiki, kuma za su yi kokari domin neman lambobin zinariya cikin gasannin kwallon PingPong, da kwallon badminton, da kwallon boli wato Volleyball ta mata, da tseren keke, da dai sauransu.
|