Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-13 14:35:11    
Mutanen Kasar Sin dake kasashen waje sun nuna yabo ga 'yan wasannin kasar Sin

cri

A cikin kwanakin da suka wuce, sabo da yawan lambobin da kungiyar wakilan kasar Sin ta samu ya yi ta karuwa, sai mutanen kasar Sin dake kasashen waje suka soma bayyana cewa, 'yan wasannin kasar Sin sun yi kyau a cikin gasanni, sabo da haka, mutanen kasar Sin dake kasashen waje sun ji alfahari sosai.

A lokacin da mataimakin shugaban babbar kungiyar mutanen kasar Sin dake birnin Barcelona ta kasar Spain Dai Huadong ya gana da manema labaru, ya ce,

" Na yi zumudi sosai. A kwanakin da suka wuce, dukkanmu mun yi hira a kan lambobin zinariya. A kullum mun bude kamputa da dare, sai a lokacin da muke duba internet da safe ko kowane lokaci, za mu iya ganin labarun gasar Olympic ta Beijing.

Mr. Xue Yongcai dake zama a kasar Singapore ya mai da hankali sosai a kan gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ya ce, a lokacin da yake kallon labarun Gasar Olympic ta TV, ya mai da hankali sosai a kan 'yan wasannin kasar Sin.(Asabe)