Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 14:26:15    
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun sa ido kan wasannin Olympic na Beijing

cri

Ran 8 ga watan Agusta, an kaddamar da gasar wasannin Olympic ta Beijing a karo na 29 a birnin Beijing. A cikin 'yan kwanankin da suka gabata, kafofin watsa labaru na kasashen waje sun ba da labaru da dama game da lamarin.

Tashar internet ta Allafrica ta ba da labari cewa, gasar wasannin Olympic ta yanayin zafi a karo na 29 da ake yi a cikin kasar Sin ta kawo wa 'yan wasa na kasashen Afirka damar nuna karfinsu ga duk duniya.

Kuma a cikin labarin an nuna babban yabo ga bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, inda aka nuna cewa, wannan bikin yana kunshi abubuwa da yawa, kuma ya jawo hankulan mutane sosai. An bayyana taken wasannin Olympic na wannan karo, wato 'Duniya Daya Mafarki Daya' yadda ya kamata.

Ran 11 ga wata, jaridar Lianhe Zaobao ta Singapore ta ba da labaru da dama, inda ta nuna babban yabo ga wasannin Olympic na Beijing da sakamakon da aka samu cikin shekaru 30 na bude kofa ga kasashen waje.

Kuma Mr Cai Yiru, shehun malami na cibiyar Zhongshan ta jami'ar al'adun kasar Sin ta Taiwan ya rubuta wani bayani a wannan jarida cewa, kaddamar da gasar wasannin Olympic a birnin Beijing wannan lamarin taya murna da kuma tunawa ne ga duk mutanen kasar Sin da ke cikin gida ko kuma a kasashen waje. Wannan tabbaci ne ga karfin kasar Sin, kuma mafarki ne na jama'ar Sin zuriya bayan zuriya cikin shekaru darurruwa.(Fatima)