
Ran 11 ga wata kamfanin dillancin labaru na Algeria ya ba da labari cewa, shugaba Abdelaziz Bouteflika na kasar Algeria ya bayyana cewa, an sami babbar nasarar bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing.
Labarin ya bayyana maganar Mr Abdelaziz Bouteflika cewa, gagarumin bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ya sami yabawa daga duk duniya. Kamar sakamakon da kasar Sin ta samu a sauran fannoni, nasarar bikin bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ta bayyana cewa manufofin da shugabannin kasar Sin suka dauka suna dacewa sosai.

Mr Abdelaziz Bouteflika ya bayyana cewa, zuwa watan Disamba na shekarar bana, za a cika shekaru 50 na kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Algeria. Yanzu dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu tana bunkasuwa cikin hali mai kyau. Kuma suna da kyakkyawar makomar hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da masana'antu. Yana sanya ran ga makomar dangantakar tsakanin kasashen Sin da Algeria.(Fatima)
|