Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 14:16:27    
Yan wasan motsa jiki na kasar Kenya sun share fage sosai wajen samun lambar zinari

cri
A ran 11 ga wata, a gogon wurin, yawan yan wasan motsa jiki na kasar Kenya da za su shiga gasar wasannin Olympic na Beijing sun bar kasar zuwa kasar Sin, kafin suke tashi, sun bayyana a birnin Nairobi cewa, sun share fage sosai wajen samun lambar zinari.

Babban malamin tawagar yan wasan motsa jiki na kasar Kenya Mr. Julius Kirwa ya gayawa manema labaru kafin tafiyarsa a dakin wasan motsa jiki na kasar dake birnin Nairobi kafin tasowarsu cewa, ba mu da damuwa game da yanayin Beijing, sabo da kafin mu je birnin Beijing, mun yi tattaunawa sau da dama da wadansu yan wasan motsa jiki da suka riga suka kai birnin Beijing, sun gaya mana cewa, yanzu, yanayin Beijing yana da kyau, dalilin yanayi ba zai kawo illa ga yan wasan motsa jiki namu ba. Ya zuwa yanzu, tawagarmu, da yan wasan motsa jikinmu dukkansu suna cikin hali mai kyau, mun riga mun share fage sosai wajen samun lambar zinari a Beijing.

Yan wasan motsa jiki da suka kama hanyarsu zuwa birnin Beijing sun hada da yan wasan motsa jiki a fannonin wasan gudun tsawon mita 800 na maza, da wasan gudun tsawon mita 5000 na maza, da wasan gudun tsawon mita 10000 na maza, da wasan gudun tsawon mita1500 na mata, da wasan gudun tsawon mita 5000 na mata, da wasan gudun Marathon na mata, da dai sauran fannoni. Yan wasan gudun Marathon na maza za su iso birnin Beijing a ran 16 ga wata. (Zubairu)