Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 20:54:42    
Kafofin watsa labaru na kasashe daban daban sun yabawa wasannin Olympics na Beijing

cri
Tun bayan da aka bude bikin wasannin Olympics na Beijing, a 'yan kwanakin da suka wuce, kafofin watsa labaru na kasashe daban daban sun bayar da labaru da yawa kan wasannin Olympics na Beijing, da bikin bude wasannin, kuma sun nuna yabo sosai a kai.

Ba muhimman kafofin watsa labaru da yawa na kasar Amurka sun yabawa gaggarumin bikin bude wasannin kawai ba, har ma sun yi yabo cewa, wasannin Olympics na Beijing ya nuna hasashen Olympics,

Jaridar siyasa ta kasar Yemen ta bayar da labari a ranar 9 ga wata, inda ake ganin cewa, shirya wasannin Olympics na Beijing ya bayyana tasowar kasar Sin, da karfinta a fannin tattalin arziki, a waje daya kuma ya kara matsayin kasar Sin a duniya.

Manyan jaridu na kasar Uganda, wato jaridar New Vision, da ta Monitor sun yi bayani daya bayan daya a ranar 10 ga wata, inda suka ce, bikin bude wasannin Olympics na Beijing ya nuna dogon tarihin kasar Sin, da kuma kyakkyawar fuska ta zamanin yau. Lallai wannan wani gaggarumin biki ne. (Bilkisu)