Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 16:08:08    
Shugaban kasar Seychelles ya yaba wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
A ran 10 ga wata, Mr Michel, shugaban kasar Seychelles ya bayyana cewa, an yi bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara, kuma an burge jama'ar duniya.

Mr Michel ya koma birnin Victoria, babban birni na kasar Seychelles a ran 10 ga wata bayan ya halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing, lokacin da ya zanta da maneman labaru na kasar, ya bayyana cewa, a birnin Beijing, ya ji dadi da ya gana da shugaban kasar Sin Hu Jintao, kuma ya halarci bukukuwa kan gasar wasannin Olympics da gwamnatin kasar Sin ta shirya.

Mr Michel ya ce, ziyararsa ta Beijing ta kara zumuncin da ke tsakanin 'yan wasa na kasar Sin da na kasar Seychelles kuma tsakanin kasashen nan biyu, kuma ba za a manta da wannan ba har abada. Yana fatan za a yi gasanni na wasannin Olympics cikin nasara, kuma 'yan wasa na kasar Seychelles za su sami nasara a gasannin.(Zainab)