Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 14:15:02    
Kafofin watsa labaru na kasar Uganda sun yaba wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
Manyan jaridu 2 na kasar Uganda sun ba da labari a ran 10 ga wata, inda suka yaba wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing mai burge jama'a, kuma bikin ya shaida tsawon tarihi na kasar Sin da halin da ke ciki a yanzu.

Babbar jarida ta farko ta kasar Uganda wato jaridar New Vision ta yaba wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing mai kyaun gani. A cikin sharhin da ta bayar, an ce, duk duniya ta jira wani bikin budewa na musamman, amma bikin da birnin Beijing ya shaida wa jama'a ya wuce tsammani.

Babbar jarida ta biyu ta kasar Uganda wato jaridar Gaskiya ta bayar da wani labari a shafin wasan motsa jiki a wannan rana cewa, bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing ya shaida tsawon tarihin kasar Sin da halin da kasar Sin ke ciki a yanzu da kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, wannan shi ne wani gagarumin biki.(Zainab)