Ran 8 ga wata da dare, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Costa Rica ya kira gagarumin biki a San Jose domin taya murnar cimma nasarar bude gasar wasannin Olympic na Beijing. Jami'an gwamnati da mutanen sassan masana'antu da cinikayya da na al'adu da na tarbiyya na kasar Costa Rica da kuma hukumomin da kasar Sin ta zuba jari da wakilan mutanen Sin da ke kasashen waje fiye da 400 sun halarci wannan biki.
A cikin jawabinsa, Mr Wang Xiaoyuan, jakada na ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Costa Rica ya bayyana cewa,domin cimma mafarkin shekaru dari, jama'ar Sin sun yi namijin kokari kuma sun haye wahaloli a jere, sabo da suna fatan za su gabatar da wata gasar wasannin Olympic mafi kyau ga duk duniya.
Mutanen Sin da ke kasashen waje sun bayyana bi da bi cewa, kyakkyawan bikin bude gasar wasannin Olympic na Beijing ya shaida wata kasar Sin ta zamani mai bunkasuwa da karfi da kuma zaman lafiya ga duniya, sabo da haka mutanen Sin da ke kasashen Waje sun yi alfarma da fari ciki kwarai.(Fatima)
|