Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-10 21:53:33    
Shugabannin wasu kasashe sun nuna babban yabo a kan yadda Beijing ta share fagen wasannin Olympics da bikin fara wasannin

cri
Kwanan baya, bi da bi ne wasu shugabannin kasashen waje wadanda suka zo birnin Beijing don halartar bikin fara wasannin Olympics, suka bayyana cewa, Sin ta kammala share fagen wasannin Olympics cikin nasara da kuma inganci, kuma bikin na da ban sha'awa kwarai da gaske.

Mataimakin shugaban kasar Kenya, Kalonzo Msyoka, ya ce, bikin fara wasannin Olympics na Beijing abin al'ajabi ne, wanda ya shaida wa duniya juriyar Sinawa da iyawarsu wajen gudanar da harkoki.

Firaministan kasar Myanmar, Thein Berisha ya ce, bikin fara wasannin Olympics na Beijing na da nasara da kuma ban sha'awa sosai, kuma ya fi samun nasara a tarihin wasannin Olympics. Ya ce, bikin ya nuna cewa, tabbas ne za a sami cikakkiyar nasarar gudanar da wasannin Olympics na Beijing.

Sa'an nan, shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai ya ce, bikin fara wasannin Olympics na Beijing yana da kayatarwa sosai, kuma fasahohin zamani da aka yi amfani suna da ban mamaki, bayan haka, yadda jama'ar kasar Sin ke karbar baki da hannu biyu biyu shi ma ya burge jama'a sosai.(Lubabatu)