Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-10 17:04:18    
Babban yabo daga kafofin yada labarai na wassu kasashe ga bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Kwanan baya dai, kafofin yada labarai na kasashe daban-daban sun bayar da labarai da yawa, inda suka nuna babban yabo ga bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing da aka gudanar shekaranjiya da dare.

Jaridar 'Lianhe Zaobao' ta Singapore ta buga wani sharhin cewa, lallai bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing ya ba wa masu kallo daga kasashen yammacin duniya mamaki kwarai da gaske, inda suka kara samun ilmi a game da al'adun tsohon zamani na kasar Sin ; A lokaci guda, bikin bude wasannin ya samu amincewa sosai daga masu kallo na ciki da wajen kasar Sin.

Ban da wannan kuma, wassu muhimman kafofiin yada labarai na kasar Amurka sun sha bayar da labarai jiya Asabar, inda suka bayyana bikin bude gasar wasannin Olympics a matsayin nunin al'adun kasar Sin. Jaridar New York Times ta ce, kasar Sin dake cikin halin annashuwa ta marabce zuwan wannan gagarumar gasa a karshe. Kazalika, kamfanin watsa labaru na NBC ya ce, wadanda suka yi kallon bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing a cikin kasar Amurka ta gidan telebijin na Beijing sun fi yawa idan aka kwatanta su da na sauran bukukuwan bude wasannin Olympics da aka gudanar a waje da kasar ta Amurka.

Jaridar da ake kira 'Financial Times' ta Burtaniya ta ce, bikin bude gasar wasannin ya riga ya sa kasar Sin ta samu wata lambar yabo ta zinariya yayin da take takarar gudanar da bikin bude wasannin Olympics.

Dadin dadawa, kafofin yada labarai na kasashen Nigeria, da Massar da kuma Morocco da dai sauransu su ma sun bayar da labarai a lokaci na farko, inda suka buga babban take kan wannan gagarumin bikin bude gasar waannin Olympics ta Beijing.. ( Sani Wang)