Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-08 22:39:08    
(Sabunta)Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yi maraba da gasar wasannin Olympic na Beijing

cri
A kwanakin nan, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun bayar da labarai da yawa game da gasar wasannin Olympic na Beijing da za a yi, yadda za a yi bikin budewa, da batun wanda zai zama mai mika wutar na karshe, har ma batun wanda zai samu lambar zinari ta farko, dukkansu su zama labarai mafi jawo hankulan mutane.

Kwanakin nan, kamfanin dillancin labaru na "Itar-Tass", da na "RIA Novosti News Agency", da dai sauran kamfanonin watsa labaru na kasar Rasha sun bayar da labarai da kalmomi, da na hotuna, da na Vedio, da dai sauran hanyoyin daban daban game da gasar wasannin Olympic na Beijing. Sauran manya jaridu na kasar Rasha kuma sun bayar da labarai game da harkokin tawagar 'yan wasan motsa jiki na kasar Rasha, kamar yadda suka sauka birnin Beijing, da shiga kauyen wasannin Olympic, da dai sauransu, kuma sun nuna yabo ga kyakkyawan hali da gidaje da hidimar abinci na kauyen wasannin Olympic ke ciki. Manyan gidajen talebijin na kasar Rasha sun tura tawagoginsu zuwa birnin Beijing, don bayar da labarai game da gasar wasannin Olympic na Beijing.

Jaridar "L'equipe", jarida wadda ta shahara sosai game da wasannin motsa jiki a kasar Faransa, ta kebe shafinta na musamman a watan Yuli, don gabatar da ajandar gasar wasannin Olympic, da yan wasan motsa jiki da za su samu damar samun lambar zinari. A cikin wani bayani game da za a yi bikin budewar, an ce, shirin da Zhang Yimou ya jagoranci game da yadda yin bikin budewa, da hotuna da aka dauka lokacin da yara kanana daga kasa da kasa suke dariya, da wasan wuta, da yadda yan wasan motsa jiki za su shiga filin motsa jiki, sun zama abubuwa mafi jawo hankulan mutane guda 4.

A ran 7 ga wata, jaridar "Reforma" ta kasar Mexico ta bayar da bayani na musamman a kan halin mafi dumi-dumi da aikin shirin gasar wasannin Olympic na Beijing ke ciki, da halin aikin shiri da yan wasan motsa jiki na kasa da kasa ke ciki. Wani bayani mai suna "Sabon birnin Beijing" ya furta cewa, an hada al'adun gargajiya na kasar Sin da bunkasuwar zaman rayuwa na zamani gaba daya, wannan ya sa birnin Beijing ya zama birni mafi jawo hankulan mutane a cikin wadansu birane da suka shirya gasar wasannin Olympic a cikin shekaru nan. Birnin Beijing ya cika alkawarinsa game da gasar wasannin Olympic, kuma ya riga ya gama dukkan ayyukan shirya gasar wasannin Olympic.

Ban da wannan kuma, jaridar "Sin Chew Daily" ta kasar Malaysiya, da jaridar "Lianhe Zaobao" ta kasar Singapore, da kamfanin dillancin labaru na kasar Jamus, da jaridar "Yonhap Presse Agentur" na kasar India, da jaridar "Asia News Time" na kasar Tailand, da jaridar "Tuoi Tre" na kasar Vietnam, da jaridar gwamnatin kasar Nepal, wato jaridar "The Rising Nepal", da jaridar "Katmandu Post", dukkansu sun bayar da labaru don maraba da gasar wasannin Olympic na Beijing. (Zubairu)