Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-31 09:25:20    
Tawagar gudun ba da sanda ta mata ta kasar Nijeriya ta yi sa'ar samun dama ta karshe ta shiga gasar wasannin Olympic

cri
Sabo da tawagar gudun ba da sanda mai tsawon mita 400 a tsakanin yan mata hudu ta kasar Finland da ta kasar Cuba sun janye daga gasar wasannin Olympic ta Beijing bi da bi, don haka, tawagar gudun ba da sanda ta mata ta kasar Nijeriya ta samu dama ta karshe ta shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing.

Bisa labari da kamfanin watsa labaru na kasar Nijeriya ya bayar, an ce, kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya wato IAAF ta riga ta aika wasika zuwa kwamitin wasannin Olympic na kasar Nijeriya, inda ta gayyaci tawagar gudun ba da sanda ta mata ta kasar Nijeriya da ta shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing.

A gaskiya dai, tawagar gudun ba da sanda mai tsawon mita 400 a tsakanin yan mata hudu ta kasar Nijeriya tana da karfi sosai, sun taba cin lambar yabo ta tagulla a cikin gasar wasannin Olympic ta Sydney ta shekarar 2000. Amma, sabo da ba su shiga gasannin tattara maki da yawa don shiga gasar wasannin Olympic ba, shi ya sa, ba su samu izinin shiga gasar wasannin Olympic cikin wa'adin da kungiyar IAAF ke tsara ba.

Yanzu, tawagar da ake sa rai sosai ta samu damar shiga gasar wasannin Olympic, sabo da haka, jama'ar kasar Nijeriya su sake fatan tawagar za ta iya samu lambar yabo ta gasar wasannin Olympic nan. (Zubairu)