Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 16:39:27    
MDD tana fatan gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta iya samun babbar nasara

cri
Lokacin da Willi Lemke, manzon musamman na babban sakataren MDD a fannin wasannin motsa jiki ke zantawa da kafofin watsa labarai na kasar Jamus a ran 29 ga wata, ya bayyana cewa, MDD tana fatan gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta iya samun babbar nasara, kuma dukkan kasashen duniya za su iya shiga gasar cikin lumana.

Mr. Lemke ya bayyana cewa, ya riga ya amince da gayyatar da shugaba Rogge na kwamitin wasannin Olympics na duniya ya yi masa, kuma zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta Beijing. Ban da wannan kuma yana ganin cewa, zargin da mutane kalilan suka yi wa kasar Sin ta yin amfani da gasar ya zarce abubuwan da aka tanada a fannin wasannin motsa jiki. Mr. Lemke ya ce, gasar wasannin Olympics ba wani biki ba ne na 'yan siyasa, haka kuma ita ba wani babban taro ba ne na MDD. Don haka bai kamata a sanya siyasa a cikin gasa ba. (Kande Gao)