Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 14:07:24    
Jakadan kasar Sin dake Kenya ya shirya bikin fatan sauka lafiya ga kungiyar wakilan 'yan wasan Olympic da ta nakasassu na Kenya don zuwa birnin Beijing

cri
A gun liyafar da aka yi a ofishin jakada dake kasar Kenya a ran 29 ga wata, jakadan kasar Sin Zhang Ming ya shirya bikin nuna fatan sauka lafiya ga kungiyar wakilan 'yan wasan Olympic da ta nakasassu na kasar Kenya don zuwa birnin Beijing. Ya bayyana cewa:

A karkashin goyon baya da kasashen duniya, ciki har da kasar Kenya suka nuna, gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar Sin suna yin kokarin kau da wahala don sake gina yankin dake fama da bala'in girgizar kasa, kuma sun dukufa kan ba da taimako ga mutane masu fama da bala'in wajen farfado da gidajensu, a sa'i daya kuma, suna ci gaba da aikin share fagen gasar wasannin Olympic. Mun yi imani da cewa, za mu ci nasara a gun gasar wasannin Olympic da za a yi a birnin Beijing.

Bugu da kari, Mr. Zhangming ya gabatar da aikin share fage na gasar wasannin Olympic da takwasannin Olympic na nakasassu ga mambobin kungiyar wakilan ta kasar Kenya, kuma yana fatan 'yan wasanni na Kenya za su ci nasara a gun gasar.

Ministan matasa da na wasanni na kasar Kenya Helenm Sambili, mataimakin ministan harkokin waje Richard Onyonka, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Kenya Kipchoge Keino, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Kenya Douglas Sidialo da wasu 'yan wasa da za su shiga gasar wasannin Olympic da gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing su 200 sun halartar liyafar nan. Shugaban Helen Sambili ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da ta nuna goyon baya da ba da taimaka ga kasar Kenya a kan wasanni da sauran fannoni, kuma yana fatan za a samu nasara a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Asabe)