Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-30 13:58:43    
'Yan wasan Iraki sun samu izinin halartar gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri
A ran 29 ga wata, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya bayar da wata sanarwa a hedkwatarsa dake birnin Lausanne na kasar Switzerland cewa, za a mayar da damar shigar da 'yan wasan kasar Iraki a gun gasar wasannin Olympic na Beijing.

Sanarwar ta ce, kwamitin wasannin Olympic na duniya da tawagar wakilan gwamantin kasar Iraq sun daddale wata yarjejeniya, inda aka bukaci kasar Iraq da ta kafa kwamitin wasannin Olympic na wucin gadi dake zaman kansa, kuma kafin karshen watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, dole ne a kafa kwamitin wasannin Olympic na kasar Iraki a hukunce.

Bisa wannan sharadi, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya yarda da kwamtin Olympic na Iraki na wucin gadi da ya zabi yan wasanni, da masu bayar da horo, da masu jagorar tawaga, da kuma shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing. Shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Jacques Rogge ya yabo ga kokarin da gwamantin kasar Iraq ke yi domin moriyar yan wasanni, kuma ya ce, kwamitin wasannin Olympic na duniya da gwamnatin kasar Iraki dukkansu suna fatan yan wasanni na kasar Iraki su shiga cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing. (Zubairu)